Kafar watsa labaran kasar Faransa ta bayar da rahoto a ranar Alhamis cewa, kasar Faransan tana shirin janye dakarunta daga kasar Mali, bayan sun shafe watanni biyu suna yaki da masu tada kayar baya, ta yadda za su sharewa tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta hanyar maye gurbinsu.
Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta bayyana cewa, "yayin da kasar ta Faransa ke ci gaba da daukar matakan soja kan masu kishin Islama a arewacin kasar Mali, Faransan kuma tana shirin mika aikin ga MDD."
Bugu da kari ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius, ya shaida wa gidan rediyon Faransa a ranar Alhamis da safe cewa, yana sa ran, MDD za ta yanke shawarar tura tawagar wanzar da zaman lafiya zuwa kasar da ke yammacin Afirka a watan Afrilu don ganin an gudanar da zaben shugaban kasar ta Mali cikin lumana.
A kwanakin nan ne shugaban kasar ta Mali Traore Diocounda da mai rikon mukamin firaministan kasar Diango Cissoko, suka bayyana kudurinsu na gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a watan Yuli.
Idan ba a manta ba, a ranar 11 ga watan Janairu ne kasar Faransa ta fara daukar matakan soja a Mali bisa bukatar mahukuntan kasar, domin fatattakar 'yan tawaye tare da maido da ikon yankunan kasar, kuma ya zuwa yanzu, an kashe kimanin sojojin Faransa 4 a rikicin na Mali.(Ibrahim)