Sojojin kasar Burkina Faso dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MISMA a kasar Mali, sun karbi tuta daga sojojin kasar Faransa a ranar Talata a birnin Tombouctou dake arewacin kasar Mali a wani labari da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu. An yi bikin mika tutar ne a Tombouctou a gaban idon babban kwamandan sojojin Faransa Serval, janar De Saint Quentin, da na tawagar MISMA 'dan kasar Najeriya, janar Shehu Abdulkadir da kuma manyan jami'an sojojin kasashen Mali da Burkina Faso.
A lokacin da yake yabawa da ayyukan da sojojin kasar Mali suka yi, na Afrika da na Faransa, janar De Saint Quentin ya bayyana cewa, mun nuna jaruntaka da niyya, da tabbatar da cewa, kasar Mali tana iyar kawo karshen duk wasu kungiyoyin kishin Islama dake neman hadasa tashe-tashen hankali a tsakanin al'ummomin kasar Mali dake neman rayuwa cikin zaman lafiya.
Ana sa ran kwamandan rundunar sojojin Burkina Faso, janar Nabere Honore Traore zai kwantar da hankalin mutanen birnin Tombouctou ta hanyar tura sojojin kasarsa 650 a wurin.
Kana kuma wadannan sojoji 650, an tanadar musu kayayyakin aikin da suka hada da motocin yaki, manyan makamai, motocin likita da sauransu, a cewar wata majiyar tsaro. Kuma a cewar wannan majiya, za a tura sojojin kasar Faransa dake Tombouctou zuwa birnin Gao dake arewa maso gabashin kasar Mali. (Maman Ada)