in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falesdinu za ta mika rokon shiga M.D.D a watan Satumba na shekarar bana
2011-08-14 17:34:00 cri
A ran 13 ga wata, wani babban jami'in gwamnatin Falesdinu ya bayyana cewa, bangaren Falesdinu za ta mika rokon shiga M.D.D yayin shirya babban taron M.D.D a karo na 66 a watan Satumba na shekarar bana.

Mamban kwamitin gudanarwa na kungiyar PLO Ahmed Majdalani ya bayyana cewa, tawagar da ke karkashin jagorancin shugaban kungiyar PLO Mahmoud Abbas za ta halarci babban taron M.D.D da za a shirya a watan Satumba na bana, kuma Mahmoud Abbas zai mika rokon shiga M.D.D ga babban sakataren majalisar, Ban Ki-Moon. A wannan lokacin ne kuma, Mahmoud Abbas zai bayar da jawabi, sannan kuma zai yi kira ga kasashe mambobin M.D.D da su nuna goyon baya ga bangaren Falesdinu da ya shiga majalisar.

A farkon watan Satumba na shekarar bara, bangarorin Falesdinu da Isra'ila sun yi shawarwari kai tsaye a birnin Washington, amma an yi watsi da shawarwarin saboda kasar Isra'ila ba ta yarda da shirin kayyade kafa matsugunan Yahudawa a yankin da ke yammacin kogin Jordan ba. A watan Yuni, kungiyar PLO ta sanar da cewa, a watan Satumba na bana, za ta mika rokon ta na shiga M.D.D da kuma rokon M.D.D da ta amince da kasar Falesdinu.(Abubakar)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China