in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PMI na kamfanonin kira na Sin ya haura kashi 50 bisa dari cikin watanni uku da suka gabata
2013-01-01 12:08:28 cri
Yau Talata 1 ga watan Janairu, kungiyar kula da harkokin sayayya da kuma sufurin hajoji ta kasar Sin, da cibiyar sa ido kan sassan gudanar da ayyukan hidima ta hukumar kididdigar Sin sun bayyana cewa, fihirisar manaja mai saye watau PMI, ta kamfanonin kira na Sin ta kai kashi 50.6 bisa dari a watan Disamba na shekarar 2012, kuma fihirisar ta yi dai dai da na watan Nuwamba, hakan ya sa fihirisar manaja mai saye ta yi sama da kashi 50 bisa dari cikin watanni uku na karshen shekarar bara.

Yayin da yake amsa tambayoyin da manema labarai suka yi masa, mataimakin shugaba na kungiyar kula da harkokin sayayya da kuma sufurin hajoji Cai Jin ya bayyana cewa, tun watan Satumba na bara, fihirisar ke ci gaba da samun karuwa har zuwa karshen watanni uku na bara inda ta haura kashi 50 bisa dari, lamarin da ya nuna farfadowar tattalin arzikin kasar, wanda matakin ya zamo mai kyau ga gudanar harkokin tattalin arzikin kasar a shekarar 2013.

Amma wani masani dake cibiyar nazarin ci gaban kasa a majalisar gudanarwa ta Sin Zhang Liqun ya nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasar yana tafiyar hawainiya, inda hajojin da ake fitarwa zuwa ketare bisa bukata ya ragu kadan, lamarin da ya nuna, har yanzu yanayin fitar da hajojin kasar zuwa ketare bai kai yadda ake fata ba, amma sabo da karuwar ayyukan zuba jari da yawan hajojin da aka sayar a cikin gida, karfin bukatun kasuwannin kasar zai sami karko. Sakamakon haka, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 7 bisa dari, ko kashi 8 bisa dari, kuma watakila ne yanayin karuwar tattalin arzikin zai sami karko yayin da ya kai wannan adadi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China