Game da wannan batu da kungiyar LAS ta yi a ranar 26 ga watan Maris, a kwanan baya, yayin da yake magana da kafofin yada labaru na Turkiya, Bashar al-Assad ya yi nunin cewa, a hakika , matakin da aka dauka ba shi da wani tushe a fannin doka.
A cewar shugaban,kungiyar tana wakiltar kasashen Larabawa ne, a maimakon Larabawa, kuma Kungiyar LAS, bisa doka, ba ta da ikon bayarwa ko kuma kwace ikon wata kungiya.
Bugu da kari, Bashar al-Assad ya yi gargadin cewa, idan an yi juyin juya hali ko kawo baraka ga kasar Syria,hakan zai kawo babbar illa ga tsaron shiyya-shiyya, kuma za a shiga yanayin rashin tabbas a kasashe makwabtanta, da ma yankin Gabas ta Tsakiya baki daya har na tsawon sama da shekaru 10 masu zuwa.(Fatima)