Yayin da yake ganawa da membobin tawagar rukunin kula da ayyukan kasashen Amurka da Sin ta majalisar wakilan kasar Amurka a wannan rana a birnin Beijing, janar Chen Bingde ya ce, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, gami da dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan na samun manyan sauye-sauye, don haka Sin na fatan kasar Amurka za ta dauki matakan da suka dace domin kawar da abubuwan dake jawo cikas ga ci gaban dangantakar kasashen biyu.
A nasu bangaren, shugabannin tawagar rukunin kula da ayyukan kasashen Amurka da Sin ta majalisar wakilan kasar Amurka Mista Charles Boustany da Rick Larsen sun bayyana cewa, rukunin zai ci gaba da kokari wajen kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka gami da sojojinsu.(Murtala)