A ran 2 ga wata, wakilan kungiyar sada zumunta don yada al'adun al'ummar Sin wadanda suke karkashin jagorancin Cai Wu sun isa yankin Taiwan, kuma za su halarci taron dandalin musayar al'adu a tsakanin bangarori biyu da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan da za a yi a ran 6 ga watan Satumba.
A gun liyafar dare da Mr. Shen Qingjing, shugaban asusun al'adu da ilmi na Shen Chunchi na Taiwan ya shirya musu a birnin Taipei, Mr. Cai Wu ya ce, dalilin da ya sa wakilan kungiyar sada zumunta don yada al'adun al'ummar Sin suka kai wa yankin Taiwan ziyara shi ne suna son samun ra'ayi daya da shawarwarin da za a bayar domin kokarin mayar da su kan manufofin yin musayar al'adu da za su iya kawo wa 'yan uwa hakikanin moriya da ke zaune a tsakanin bangarori biyu. (Sanusi Chen)