A yayin ganawar, Yu Zhengsheng ya ce, kasar Sin na son yin kokari tare da bangaren Turai wajen zurfafa dangantakar abokantaka da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni bisa tushen girmama juna, amincewa da juna, yin hadin gwiwa da samun nasara tare, a kokarin kawo wa jama'ar Sin da Turai alheri, da ba da kyakkyawan tasiri a duk duniya baki daya ta fuskar samun zaman lafiya da wadata. Kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan bunkasa nahiyar Turai bai daya, da kuma kokarin da kasashen Turai suke yi wajen tinkarar matsalar bashin da ke addabarsu.
A nata bangaren kuma, madam Ashton ta ce, kasar Sin, aminiya ce mai karfi ga kungiyar EU da ke kokarin jure wahala da farfado da tattalin arziki. Inganta hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban yana samar da amfani wajen raya bangarorin 2 duka. Bangaren Turai na son kara raya huldar abokantaka da ke tsakaninsa da Sin bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.(Tasallah)