Yu Zhengsheng ya kara da cewa, wajibi ne a nace kan hanyar raya tsarin siyasar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, don haka bai kamata a koyi tsarin siyasa na Turawa ba. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, kamata ya yi a raya tsarin demokuradiyya irin na gurguzu, da sa kaimi wajen ba da shawarwari ga ayyukan jam'iyyar da gwamnatin, tare da nuna goyon baya wajen biyan bukatun da sauraron ra'ayoyin jama'a, da sa kaimi wajen yin mu'amala da tattaunawa, don fadin gaskiya game da hakikanin halin da kasar ke ciki.
Taron da aka yi na wannan karo ya kasance taron farko na majalisar CPPCC karo na 12 cikin shekaru 5 masu zuwa. Mambobi sama da 2200 sun zabi shugaban majalisar da mataimakansa da sauransu, kana kuma sun tattauna tare da ba da shawarwari game da batutuwan siyasa, tattalin arziki, zaman rayuwar al'umma da sauransu. Bisa kididdigar da aka samu, an ce, mambobin majalisar sun ba da shawarwari da yawansu ya kai sama da 5000, abubuwan da ke kunshe a ciki sun hada da inganta ayyukan kiyaye muhalli, da yunkurin ayyukan zamani a birane da kauyuka, da karfafa aikin yin gyare-gyare kan tsarin siyasa na kasar.(Bako)