Kungiyar tarayyar Turai (EU) na fatan ganin tura jojojin kasa da kasa a Mali, wanda shirin ya samu amincewa, za'a gaggauta ba da izni kansa daga kwamitin tsaro na MDD, a cewar wani sakamakon karshen taron ministocin harkokin wajen kasashen Turai da ya gudana a ranar Litinin a birnin Brussels.
Ministocin harkokin wajen tarayyar Turai sun yaba wa ayyukan da kungiyar ECOWAS da AU suka gudanar a wannan fanni wadanda suka taimaka wajen amincewa da matakin dubarar tura sojoji.
Haka kuma ministocin sun bayyana muhimmancin taimakon kudin da ya dace kan wannan shiri na Afrika game da kasar Mali daga wajen kasashe da kungiyoyin shiyyar, da ma kungiyoyin kasa da kasa masu ba da tallafinsu sosai.
Taron kuma ya jaddada cewa, rikicin siyasa da na tsaro a kasar Mali na bukatar wani hadin kai mai fa'ida da karfi, ta yadda za'a samu mafita cikin dogon lokaci, wadda a cikinta matsayin Afrika ya zama wajibi.
Daga karshe, ministocin harkokin wajen tarayyar Turai sun sake maimaita kiransu ga hukumomin kasar Mali da su gabatar cikin gajeren lokaci da jadawalin aiki mai nagarta da zai samu amincewar bangarori daban daban domin maido da tsarin kundin mulki da na demokaradiyya, har ma da binciken fararen hula daga jami'an tsaro. (Maman Ada)