in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nasarar kasar Sin na dacewa da babbar moriyar kungiyar EU, in ji shugabannin kungiyar
2012-10-20 17:50:22 cri
Shugabannin kungiyar EU sun bayyana a ranar Jumma'a 19 ga wata a birnin Brussels cewa, nasarar da kasar Sin ta samu na dacewa da babbar moriyar kungiyar. Kungiyar EU kuma za ta mai da hankali kan bunkasa dangantaka tsakaninta da kasar Sin cikin dogon lokaci.

A wannan rana, yayin da yake ganawa da manema labarai bayan kammala taron kolin kungiyar tarayyar Turai a lokacin kaka, shugaban majalisar tarayyar Turai Herman Van Rompuy ya bayyana cewa, kamata ya yi kungiyar EU ta sa ido tare da yin hangen nesa a yayin da take kokarin bunkasa dangantaka tsakaninta da kasar Sin. Ya ce, nasarar kasar Sin na dacewa da babbar moriyar kungiyar EU cikin dogon lokaci. Daga lokacin bazara na badi kuma, kungiyar za ta fara shirya ganawa tsakanin shugabannin Sin da na kasashen Turai karo na 16 da za a yi a lokacin kaka na shekarar 2013 a kasar Sin yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaban hukumar kungiyar EU Jose Manuel Durao Barroso ya furta cewa, a gun taron kolin da aka kammala, shugabannin kungiyar EU sun yi shawarwari kan dangantaka tsakaninsu da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. Ya ce, dangantaka irinta moriyar juna tsakanin bangarorin biyu, mihimmin abu ne da zai tabbatar da bunkasuwar kungiyar EU da kasar Sin, har ma duniya baki daya. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, za a samu karin ci gaba a fannin cinikayya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China