Mr. Li Ganjie, mataimakin ministan tsaron yanayin duniya na kasar Sin ya fadi haka ne a yayin taron kara wa juna sani mai take "Kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka wajen neman ci gaban tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba" da aka shirya yau 16 ga wata a nan birnin Beijing.
Sannan Mr. Li ya ba da shawarar kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka wajen neman ci gaba a fannoni daban daban ba tare da gurbata muhalli ba a inuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka bisa sakamakon da suka samu yanzu. Haka kuma, ya kamata su kirkiro sabuwar hanyar yin hadin gwiwa a fannonin kiyaye muhalli, tabbatar da lambunan tsaron yanayin duniya, samar da kayayyaki ba tare da gurbata muhalli ba. Bugu da kari, ya kamata su kara yin hadin gwiwa a fannin samar da ayyukan tsaron yanayin duniya misali irin na koyo. A waje daya, ya kamata su kara yin mu'amala da tattaunawa wajen tsara manufofin tsaron yanayin duniyarmu. (Sanusi Chen)