Musyoka ya yi wannan kalami ne a wurin kammala wani taro na tsawon mako guda da daliban kasar suka gudanar tare da tallafin kungiyar Green Friends Foundation, inda ya kara da cewa, kasar Kenya na iya amfani da bangaren shakatawa da yawon buda ido domin samar da wata hanya ta daban ta tattalin arziki.
"Garin Nairobi a kasancewar shi ta zama birni mai ni'ima a cikin yankin, kamata ya yi mu maido da abun da muka yi hasara daga birnin ta kokarin kara kare muhalli", kamar yadda ya sake jaddadawa.
Taken da aka ba wannan tsari shi ne, "yaro guda icen bushiya guda, al'umma guda kasa guda", inda matasan kasar Kenya za su kasance a tsanake domin fuskantar dukan wata matsala a cikin al'umma ta fannnin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa, da jin kai a lokacin da take kawo kalubale ga hadin kan 'yan kasar.
A lokacin wannan sabga, dimbin yara sun shuka itace domin nuna hadin kai ta hanyar kariyar muhalli, inda aka bada takardun yabo ga wadanda su ka gudanar da aikin ta hanyar mafi kyau.(Abdou Halilou ).