Mista Tondossama ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake hira da manema labarai kan filayen daji masu alfarma da aka kare a kasar, wadanda kuma suke da muhimmanci wajen ba da sha'awa ga jama'a, suna iya jawo hankalin jama'a zuwa yawon shakatawa da bude ido a kasar ta Cote d'Ivoire. Babban wurin shan iska na kasar da ke arewa masu yammacin Abidjan da kuma wani na daban da ke yammacin kasar suna kunshe da dimbin albarkatun daji da suka shafi itace da dabbobi daban daban. Babban wurin shan iska na kasar da ke yammacin kasar ya kasance daji mafi girma a yankin yammacin Afrika, wanda ke da fadin eka 636000. Kare muhalli da kuma tabbatar da kasancewar halittu daban daban a duniya sun kasance ayyuka masu muhimmanci da hukumomin kasar Cote d'Ivoire suka sa a gaban su, wadanda kuma kungiyoyi na cikin kasa da na duniya suke ci gaba da kawo kokarinsu wajen kare su daga tabarbarewa. (Abdou Halilou)