in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Faransa sun yi aniyar ci gaba da raya hulda a tsakanin kasashen 2
2013-04-25 20:12:04 cri

Ranar 25 ga wata, a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, Xi Jinping, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Faransa François Hollande, inda suka tsai da aniyar girmama juna da yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna, a kokarin ci gaba da raya huldar abokantaka a tsakanin Sin da Faransa bisa manyan tsare-tsare daga sassa daban daban.

A cikin shawarwarin, shugaba Xi ya nuna cewa, a sabon yanayin da ake ciki, wajibi ne Sin da Faransa su ci gaba da mayar da juna tamkar abokin yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, su ci gaba da mara wa juna baya, da zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Sa'an nan kuma wajibi ne su kara azama kan raya duniya cikin adalci kuma yadda ya kamata, da yin shawarwari domin warware rikicin kasa da kasa cikin lumana, a kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da samun bunkasuwa da wadata tare.

Har wa yau, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya zama dole Sin da Faransa su inganta tuntubar juna, mu'amala da juna, girmama juna da kyautata amincewa da juna. Sa'an nan ya kamata kasashen 2 su kara yin mu'amala ta fuskar al'adu, a kokarin tabbatar da kasancewar al'adu iri daban daban a duniya. Wajibi ne su kara taimakawa juna a al'amuran kasa da kasa. Kasar Sin tana sa fatan alheri kan bunkasuwar huldar abokantaka ta sabon salo a tsakaninta da Faransa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.

A nasa bangaren kuma, shugaba François Hollande ya ce, a yayin da ake fuskantar kalubaloli iri daban daban da ke shafar duk duniya, ya kamata Faransa da Sin su kara yin tattaunawa da juna, taimakawa juna, da yin hadin gwiwa a tsakaninsu, su kuma kara azama kan tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya yadda ya kamata, a kokarin kiyaye zaman lafiya da wadatuwa a duniya. Haka zalika, Faransa na himmantuwa wajen inganta huldar abokantaka da ke tsakaninta da Sin bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni ba tare da tangarda ba, bisa ka'idojin amincewa da juna da moriyar juna. Kasarsa tana girmama ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunan Sin, tare da mara wa Sin baya wajen samun ci gaba.

Bayan haka kuma, shugabannin 2 sun yi musayar ra'ayi kan yadda za a inganta hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kasashen 2 daga dukkan fannoni.

Bayan shawarwarin kuma, an rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatocin kasashen 2 da ma masana'antunsu a gaban idanun shugabannin 2. Daga bisani kuma shugabannin 2 sun ba da sanarwar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Faransa.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China