Shugaban kasar Benin dake rike da shugabancin kungiyar tarayyar Afrika AU, Boni Yayi ya fara wani rangadin aiki tun daga ranar Litinin da zai kai shi wasu kasashe goma na nahiyar Afrika domin fadakar da kasashen kan muhimmancin zaman lafiya mai karko, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Benin, Eusebe Agbangla.
"Wannan rangadin aiki na zuwa a gabannin babban taron shugabanni da gwamnatocin kungiyar tarayyar Afrika AU da zai taimakawa shugaban wannan gamayyar kasashen Afrika tare da takwarorinsa kimanta ayyukan da kungiyar AU ta yi da kuma karfafa hadin kan nahiyar wajen daidaita yake-yake domin kiyaye zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro a nahiyar Afrika da ma duniya baki daya." in ji mista Agbangla.
A cewar kakakin na ma'aikatar harkokin waje da dunkulewar Afrika na kasar Benin, shugaba Boni Yayi zai mai da hankali a yayin wannan rangadi nasa tare da takwarorinsa kan hanyoyin da za'a bi da matakan da za'a dauka domin ganin an raki fafatawa da nahiyar Afrika kan harkokin da suka shafi kasa da kasa. (Maman Ada)