A jiya Talata 11 ga wata, Thomas Donilon ya yi jawabi mai lakabin "Manufar kasar Amurka game da yankunan Asiya da tekun Fasific", inda ya bayyana manufar kasar Amurka da za a aiwatar ga kasar Sin a yayin wa'adi na biyu na mulkin shugaban kasar Barack Obama. Ya bayyana cewa, kasar Amurka ta yi maraba da bunkasuwar kasar Sin cikin lumana, kuma za ta ci gaba da dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da Sin, da warware matsalolinsu yadda ya kamata, da kuma yin kokari tare wajen inganta sabuwar dangantakarsu da dai sauransu. (Zainab)