in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Jami'in gwamnatin kasar Sin ya bukaci a karfafa tattaunawa tsakanin kasar da Amurka
2013-04-04 20:29:16 cri
Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwa ta gwamnatin Sin ya jaddada bukatar dake akwai ta inganta tattaunawa, karfafa aminci da kuma hadin gwiwa wajen aiki tare a tsakanin kasashen Sin da Amurka domin raya wata dangantaka da za ta habaka wani sabon zumunci mai mutunta ikon ko wace kasa a duniya.

Mr. Yang wanda ya fadi hakan a hirar da yayi da Sakataren harkokin kasashen wajen Amurka John Kerry ta wayar tarho a safiyar yau Alhamis, ya ce yin hakan yana da wani babban tasiri ga kasashen biyu wajen cigaba da ziyartar juna da kuma mu'amula.

Ya kuma lura da cewa dangantaka tsakanin Sin da Amurka na cikin wani sabon yanayi , don haka tana da mafari mai kyau.

A nasa bangaren Mr. Kerry ya ce, kasarsa tana matukar mutunta zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, don haka tana fatan ci gaba da wannan zumunci, sannan kuma ta karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da Sin. Ya kara da cewa, yana sa ran ziyartar Sin nan ba da dadewa sannan kuma ya yi aiki da kasar ta yadda ziyarar tasa za ta zama mai dauke da nasara.

Manyan Jami'an biyu sun yi musayar ra'ayi a kan batutuwan da suka shafi halin da ake ciki a yankin Koriya da kuma canjin yanayi.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China