in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanoni kusan dubu daya na neman hanyoyin ciniki a bikin baje kolin kasa da kasa a Aljeriya
2012-05-31 13:04:42 cri

An bude bikin baje koli na kasa da kasa a birnin Algiers na kasa Aljeriya a ranar Laraba a zauren baje koli da ke Pins Maritimes cikin yankin gabashin kasar. An samu mahalarta biki a wajen baje kolin a kalla dubu daya da suka hada da bakin kamfanoni guda 600 da kuma kamfanonin cikin gida guda 370.

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya halarci bikin bude baje kolin na kasa da kasa mai taken "shekaru 50 domin a ginawa", kamar yadda kanfanin dillancin labarai na kasar wato APS ya sanar.

Wannan bikin baje koli na kasa da kasa na kasar Aljeriya da ya kasance karo na 45, zai gudana har zuwa ranar 5 ga watan Yuni, inda aka kebe filin mai fadin murabadin mita 47160 da zai karbi kamfanoni daga kasashe 9 na turai, wasu guda 8 na yankin kasashen larabawa, 6 daga yankin arewa da kudancin Amurka, 4 kuma daga yankin Asiya da guda daya daga nahiyar Afirka.

A matsayinta na babbar kasa mai halartar bikin baje kolin, kasar Masar ta tura kamfanoni 61 a bangaren sake-sake, sinadarai da kuma ta bangaren sarrafe-sarrafe domin su halarci bikin baje kolin.

Kamfanoni na cikin gida na kasar ta Aljeriya guda 370, wadanda kashi 80 cikin 100 sun kasance kanana da matsakaitan kamfanoni, su shahara ta bangaren gine-gine, ayyukan jin dadin jama'a, ayyukan da suka shafi samar da ruwa, makamashi, noma, kayan alatu da kuma ta bangaren injiniyanci da kanikanci.(Abdou Halilou).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China