Babban mai shari'a Dr. Wily Mutunga ne ya bayyana amincewar daukacin alkalai 6 da suka jagoranci shari'ar, yana mai cewa za a fidda cikakken kofin shari'ar nan da makwannin biyu masu zuwa. Bugu da kari mai shari'a Mutunga ya ce, lokaci yayi da al'ummar kasar, da ragowar masu fada a ji, zasu hada kai domin wanzar da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkanin fadin kasar.
Kafin bayyana hukuncin da babbar kotun ta yanke, da dama daga manazarta harkokin siyasa na kallon shari'ar a matsayin irinta ta farko da aka gudanar a kasar ta Kenya, wadda ke gabashin nahiyar Afirka. Duba da cewa wannan ne karon farko da aka gudanar da shari'ar kafin rantsar da zababben shugaban kasar. (Saminu Alhassan Usman)