A ranar Lahadi 31 ga watan Maris ne babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya alkawarta taimakawa kasar Kenya da dukkanin abubuwan da suka dace, sakamakon yadda kasar ta kammala babban zabenta cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yayin wata tattaunawar da ya yi da sabon zababben shugaban kasar Uhuru Kenyatta ta wayar tarho, Ban Ki-Moon, ya yi wa gwamnati, da al'ummar kasar fatan cimma dukkanin nasarori, bisa kalubale da damammaki da kasar za ta fuskanta a nan gaba.
A yammacin ranar Asabar din da ta gabata ne dai, alkalan babbar kotun kasar ta Kenya su 6, suka tabbatar da sahihancin babban zaben da ya gabata, bisa shari'ar da aka shigar gaban kotun, wadda ta kalubalanci sakamakon, suna musu cewa, zaben ya yi daidai da tanaje-tanajen kundin mulkin kasar ta Kenya.(Saminu)