in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kafa tsari mafi girma a duniya dangane da yin kandagarkin kan girgizar kasa
2013-03-18 16:51:23 cri
Yau Litinin 18 ga wata, cibiyar nazarin kimiyyar samar da saukin radadin bala'i ta birnin Chengdu na lardin Sichuan ta gabatar da cewa, da goyon bayan ma'aikatar kula da kimiyya da fasaha, huhumar tinkarar girgirzar kasa, da sashin kula da harkokin kimiyya da fasaha na lardin Sichuan, da kuma tsarin kwararru dari daya na jihar Sichuan da sauransu, cibiyar ta kafa wani tsarin yin kandagarki kan girgizar kasa, da za ta shafi murabba'in kilomita dubu 400, wanda ya fi na kasar Japan mai murabba'in kilomita dubu 377 girma, hakan dai ya sanya tsarin na kasar Sin zama mafi girma a duniya.

An ba da labarin cewa, wannan tsari na kunshe da nu'urori 1213, da cibiyoyin yin kandagarki da dai sauran tsare-tsaren yin musayar bayanai a birane ko larduna 8 na kasar, wadanda kuma za su lashe kudin Sin Yuan miliyan 160. Haka kuma tsarin zai yi amfani ga mutane miliyan 80, da kuma hanyar dogo, da ta jiragen kasa dake karkashin kasa, da sha'anin samar da wutar lantarki ta hanyar makamashin nukiliya da sauransu dake kewayensa.

Ya zuwa yanzu, an yi aikin gwaji kan wannan tsari har fiye da sau 1200, kuma an cimma nasara wajen yin kandagarkin grigizar kasa, wadda ta abku a ran 19 ga watan Febrairu a cikin wannan shekara a lardin Yunnan, wadda kuma ta kawo babbar illa. Matakin da ya nuna cewa, an koyi darasi daga babbar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China