A yayin ganawar, Sani ya bayyana cewa, ko da yake kamfaninsa na da nisa sosai a tsakaninsa da kasar Sin, amma kullum yana mai da hankali kwarai da gaske kan girgizar kasar da ta faru a Wenchuan. A ko wace shekara ya kan ba da kyautar kudi da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 20 ga wuraren da bala'in ya shafa, bisa ga ruhun jin kai. Ya kara da cewa, shekarar bana, shekara ce ta cikon shekaru 4 da abkuwar bala'in. Manyan nasarorin da gwamnatin Sin ta samu wajen farfado da wadannan wurare bayan bala'in sun samu amincewa sosai. Farfado da wadannan wurare na bukatar dogon lokaci, don haka kamfanin zai ci gaba da bayar da kyautar kudi a nan gaba. (Tasallah)