Kungiyoyin kasashen duniya ciki har da kungiyar EU sun ba da kyautar kudi wajen raya sana'ar yin gora a lardin Sichuan, watau inda aka samu girgizar kasa, don raya sana'ar goran cikin dogon lokaci, kana, an yi amfani da fifikon na wannan lardi don rage talauci da samar da guraben aikin yi da gina gine-gine don maganin girgizar kasa da samun bunkasa cikin dogon lokaci.
Haka kuma, an kimanta cewa, wannan aiki zai kara samar da guraben aikin yi da yawansu ya kai sama da dubu 20, yanzu, an kafa yankunan masana'antu yin gora 8 a gundumomin da aka samu bala'i masu tsanani.(Bako)