in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala akasarin ayyukan sake farfado da yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a lardin Sichuan
2011-05-10 15:42:54 cri
Ranar Talata 10 ga wata, mataimakin shugaban kwamitin kula da ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin Mista Mu Hong ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, am kammala kashi 95 bisa dari na ayyukan sake farfado da yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su a shekara ta 2008 a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, kuma a watan Satumban bana za'a kammala dukkan wadannan ayyuka.

A wajen taron manema labarai da aka shirya a wannan rana a birnin Chengdu na lardin Sichuan, Mista Mu Hong ya ce, a yankunan da bala'in girgizar kasa ya shafa a larduna uku wato Sichuan, Shanxi, da Gansu, an gina gidaje sama da miliyan 1.9 a yankunan karkara, da gidaje dubu 280 a birane da garuruwa, da makarantu fiye da 3800, gami da sauran wasu abubuwan biyan bukatun jama'a na yau da kullum sama da dubu 5. Mu Hong ya ce, bayan da aka kammala ayyukan gina gidajen kwana, makarantu, asibitoci da sauran wasu abubuwan biyan bukatun jama'a na yau da kullum, yanzu ana dab da kammala sauran ayyukan farfado da lardunan.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China