Gwamnatin kasar Sin za ta samar da kudin taimako da ya kai dala miliyan guda ga yankunan da girgizar kasa ta galabaita a Turkiya
Kwanan nan, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin samar da kudin taimako da ya kai dala miliyan guda ga yankunan da girgizar kasa ta galabaita a kasar Turkiya, domin taimaka wa gwamnatin kasar da jama'arta wajen gudanar da ayyukan agaji.
A ranar 23 ga wata, girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 7.3 ta afka wa lardin Van da ke gabashin kasar ta Turkiya, bala'in da ya yi sanadiyyar hasarar rayukan jama'a da dukiyoyi da yawa.(Lubabatu)