in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen kasashen Austria da Sudan sun tattauna kan farfado da shawarwari tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu
2012-06-23 17:13:28 cri
Ranar 22 ga wata, a birnin Vienna na kasar Austria, ministan harkokin wajen kasar Sudan Ali Ahmed Karti, da takwaransa na kasar Austria kana mataimakin firaministan kasar Michael Spindelegger sun yi shawarwari, inda suka yi musanyar ra'ayi kan rikicin Sudan da Sudan ta Kudu, da cimma matsaya daya cewa, ya zama dole bangarori masu rikici da juna su sake komawa teburin yin shawarwari.

Bayan shawarwarin, Michael Spindelegger ya fadawa manema labarai cewa, ya kamata a farfado da shawarwari tsakanin bangarorin dake rikici, saboda akwai bukatar su zama cude-ni-in-cude-ka. Karti ya yarda da hakan, inda ya ce, irin wannan dangantakar dake tsakaninsu na dacewa da moriyar kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki. Ya kuma jaddada cewa, lokaci ya zo a farfado da shawarwari.

Bugu da kari kuma, Karti ya ce, abun da ya kamata a ba fifiko yanzu shi ne, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin, wato kwantar da rikici a yankin iyaka, daga baya za'a iya gudanar da shawarwari kan batun da ya shafi tattalin arziki, ciki har da batun raba albarkatun mai.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China