Mambobin kwamitin sulhu na MDD mai kasashe 15 sun fada cikin wata sanarwar da suka bayar cewa, sun yi maraba da janyewar sojojin Sudan da Sudan ta kudu daga yankin Abyei, suna masu jaddada cewa, wajibi ne janyewar ta kunshi 'yan sanda da 'yan sandan da ke kula da harkar mai.
Sanarwar ta ce, mambobin kwamitin sulhun sun yi maraba da dawowar sassan biyu kan teburin tattaunawa a ranar 29 ga watan Mayu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha karkashin kwamitin shiga tsakani na AU.
Kwamitin ya kuma karfafawa sassan biyu gwiwar ci gaba da tattaunawa, ta yadda za su warware dukkan batutuwan da suke korafi a kai karkashin kuduri mai lamba 2046.
Har ila yau, kwamitin ya bayyana damuwarsa kan "rashin samar da kafar kai kayayyakin jin kai a jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile. (Ibrahim)