Sanarwar ta ce, tashe-tashen hankali da bangarorin biyu suka tayar sun jawo asarar rayukan fararen hula da dukiya, kuma mutane da dama sun kaura daga wurarensu sannan kuma an tilasta wasu hukumomin jin kai da su bar wurin. Ban Ki-Moon kuma ya nuna matukar rashin jin dadi domin ganin cewa, an tada rikici a wani matsugunan 'yan gudun hijira dake yankin Shaeria.
Dadin dadawa, Ban Ki-Moon ya jaddada cikin sanarwar cewa, zai ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan da wasu kungiyoyi ciki har da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da AU cikin hadin kai, hukumomin MDD, kungiyoyin masu zaman kansu suka yi a yankin.(Amina)