Shugaban kwamitin sulhun na wannan wata, kuma jakadan kasar Guatemalan a MDD, Gert Rosenthal, ya karanta wannan sanarwa ga manema labaru, inda ya ce wasu dakarun da ba a tantance wanene su ba sun yi kwanton bauna ga wasu sojojin rundunar UNAMID wadanda suka yi rangadi a garin El Geneina na jihar West Darfur da ke kasar Sudan a ranar 2 ga wata, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 'yan Nijeriya 4, tare da raunatar wasu 8, don haka kasashe mambobin kwamitin sulhun sun yi tofin Allah tsine da babbar murya.
Cikin sanarwar, an kara da cewa, kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin kasar Sudan da su gagauta aiwatar da bincike kan lamarin, don gurfanar da masu laifin a gaban kotu. Ban da haka kuma, kwamitin ya sake yin bayanin cewa, zai goyi bayan rundunar UNAMID, kana ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Darfur da su hada kai tare da rundunar. (Bello Wang)