in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin ciniki da aka samu tsakanin Sin da Afirka a shekara ta 2011 ya zarce dala biliyan 150
2012-01-11 17:00:43 cri

Ranar Laraba 11 ga wata, a nan birnin Beijing, shugaban sashin kula da harkokin kasashen Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Lu Shaye ya bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekara ta 2011, yawan kudin cinikin da aka samu tsakanin Sin da Afirka ya zarce dala biliyan 150.

Mista Lu ya ce, bayan da aka kafa dandalin tattaunawa na hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka a shekara ta 2000, ya zuwa yanzu, hadin-gwiwar Sin da Afirka ta fuskokin tattalin arziki da cinikayya na bunkasa cikin sauri, kuma a shekara ta 2008, yawan kudin cinikin da aka samu tsakaninsu ya wuce dala biliyan 100 a karo na farko. Daga baya a shekara ta 2009, kasar Sin ta zama babbar aminiya ta farko ta Afirka a fannin cinikayya.

Mista Lu ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata wato shekara ta 2011, an kara inganta mu'amala da cudanya tsakanin manyan jami'ai na kasar Sin da kasashen Afirka, haka kuma shugabannin kasar Sin da na jam'iyyar kwaminis ta kasar sun kai ziyara kasashen Afirka sama da 20.

Har wa yau kuma, Mista Lu Shaye ya nuna cewa, kasar Sin na fatan ci gaba da hada kai tare da sauran kasashen duniya don gudanar da harkoki a nahiyar Afirka, a kokarin taimakawa ci gaban nahiyar yadda ya kamata.

Mista Lu ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba kasashen yammacin duniya sun bayyana fatansu na yin hadin-gwiwa tare da kasar Sin a nahiyar Afirka, kuma Sin tana son hada kai tare da su, a kokarin raya nahiyar yadda ya kamata. Amma Sin tana ganin cewa, abun da ya dace wajen gudanar da hadin-gwiwa a tsakaninta da kasashen yamma gami da kasashen Afirka shi ne, taimakawa bunkasuwar Afirka, kuma kamata yayi a samu daidaito tsakanin bangarorin uku.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China