in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayar da gudumowar hatsi mafi yawa a tarihinta ga yankin kusurwar gabashin Afrika
2011-10-24 15:58:26 cri

A jiya lahadi kamfanin dillacin labaru na kasar Sin ya ambato wani jami`in gwamnatin kasar yana tabbatar da cewa Kasar Sin ta bayar da tallafin abinici na adadin kudi sama da yuan miliyan 443.2 kwatankwacin dalar amurka miliyan 69.58 ga yankin kusurwar gabshin Afrika dake fama da matsanancin fari.

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnatin kasar ta bayar da irin wannan gudunmowa ga wata kasa tun bayan da ta zamo jamhuriyar jama'ar kasar Sin a 1949, a ta cewar Lu Shaye shugaban sashen harkokin kasashen Afrika na ma`aikatar lura da kasashen ketare na kasar Sin.

Ya ce da dadewa kasashen Afrika da kasar Sin suna taimakon juna sosai a duk lokacin da wani bala`i ya samu daya daga cikinsu, inda ya bayar da misali da lokacin da wata annoba ta afkawa yankunan Yushu da Zhouqu na kasar Sin, kasashen Afrika da dama sun jajantawa kasar Sin, sannan sun taimaka mata ta fuskoki daban daban.

Har ila yau cinikayya dake tsakanin kasar Sin da Afrika ta zarce dalar Amurka biliyan 100 a 2010 sannan kuma ta kai biliyan 79 a rabin wannan shekara da muke ban kwana da ita, lamarin dake nuna cewa cigaban yana kaiwa kashi 29.1 a ko wace shekara.

Mr. Lu Shaye ya cigaba da cewa kasashen Afrika suna daya daga wadanda suka fi amfana daga harkokin zuba jari na kasar Sin wanda yake bunkasuwa cikin sauri.

Haka kuma ya kara da cewa kasar Sin za ta cigaba da bayar da taimako ga kasashen Afrika, kamar yadda yake kunshe cikin sabbin matakan karfafa tattalin arziki tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika wadanda firayiminista Wen jiaboa ya gabatar a babban taron kyautata hadin kai tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika karo na 4 da aka gudanar a Cairo a 2009.

An dai tsara cewa a tsakanin ranar 26 zuwa ta 27 ga wannan wata a Hangzhou hedikwatar lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin za`a gudanar da taron shugabannin kwamatin kyautata hadin kai tsakanin Sin da nahiyar Afrika domin nazartar irin cigaban da aka samu wajen aiwatar da abubuwan da babban taro karo na 4 da aka gudanar a Cairo ya zartar, sannan kuma a fara shirye shiryen gudanar da makamncinsa karo na biyar a shekarar badi.

Daga bisani Mr. Lu Shaye yace babu shakka ya zuwa yanzu kasar Sin da Afrika sun samu cigaba da dama a kuma fannoni daban daban wadanda suka hadar da batun soke basussuka, cire haraji,da kuma samar da basussuka na musamman.

Sauran sune bunkasa ilimi, ayyukan gona da makamashi.

A yanzu haka kuma kasar Sin tana gudanar da ayyuka kusan dari da suka shafi makamashi mai tsabta a kasashen Afrika daban daban.(BAGWAI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China