Kasar Sin za ta cigaba da kara zurfafa dangantakarta da kasashen nahiyar Afrika ta fannoni daban daban da suka shafi ayyukan kasuwanci da na gine gine, in ji mukadashin ministan kasuwancin kasar Sin mista Li Jinzao.
Haka kuma kasar Sin na fatan kara yawaita zuba jari a Afrika a bangaren kudi, yawon bude ido, zirga zirgar jiragen sama da kuma da makamashi mista Li Jinzao ya kara da cewa, a yayin wani bikin baje kolin kasa da kasa na farko kan ayyukan kasuwanci na Beijing.
Kalaman mista Li Jinzao sun biyo bayan kiran faraministan kasar Wen Jiabao yayi kan kara bude bangaren ayyuka a duk fadin kasar Sin tare da bada kwarin gwiwa ga masu samar da ayyuka na kasar wajen shiga kasuwannin waje.
A cewar mukadashin ministan kasuwancin kasar Sin, nahiyar Afrika ta kasance wata makoma mai muhimmanci ga masu zuba jari na kasar Sin. Fiye da kamfanoni 2000 na kasar Sin suka zuba jari a wasu bangarori da dama na kasashen, daga samar da na'urorin sadarwa har zuwa na sufuri. (Maman Ada)