Babban taron MDD ya zabi kasar Kenya domin shugabantar wani gungun aiki na kasa da kasa na GTI da aka azama nauyin shirya manufofin maradun samun cigaba mai karko na ODD, in ji ministan harkokin wajen kasar Kenya a ranar Litinin.
Wata sanarwa da aka fitar a Nairobi ta nuna cewa, zaben kasar Kenya ya samu yabo da amincewa daga kasashe masu tasowa da dukkansu suke fama da muhimman kalubale ta fuskar al'umma, tattalin arziki da kuma muhalli, wannan zabe zai bai wa wannan kasa dake gabashin nahiyar Afrika damar shiga gaba wajen aiwatar da wannan manufa.
Wannan kwamitin aiki a bude yake ga dukkan kasashe mambobi 193 dake cikin MDD domin kawowa taimako, baya ga haka kuma zai kasance a karkashin wani tsari mai kunshe da kasashe 30 mambobin MDD da aka zabo daga yankuna biyar, ta yadda za'a tabbatar da shugabanci mai kyau wajen bullo da wadannan maradun samun cigaba mai karko, in ji ofishin ma'aikatar wajen kasar.
Wadannan muradu za su kasance wata hanya da wata damar bunkasa dangantakar kasa da kasa wajen kawar da talauci da kare muhalli. (Maman Ada)