Kawancen jam'iyyun siyasa a kasar Kenya karkashin jagorancin firaministan kasar Raila Odinga za su shigar da kara a kotun kolin kasar a ranar Jumma'a don kalubalantar zaben makon da ya gabata na Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban kasar na hudu.
Daya daga cikin ministocin kawancen jam'iyun Mutula Kilonzo, ya shaida wa taron manema labarai a Nairobi cewa, shaidun da suka samu da ke nuna cewa, an tabka magudi a zaben mai tarihi, da 'yan kallo na kasa da kasa suka kalla zai girgiza 'yan kasar matuka.
Ko da yake shi ma James Orengo ya ce, hukumar zabe da shata kan iyakoki ta kasar mai zaman kanta(IEBC) tana kassara kokarinsu na neman bayanai kamar yadda babbar kotun kasar ta bayar da umarni a ranar Laraba.
Shi dai Raila Odinga ya ki yarda cewa, ya sha kaye a zaben, inda yake bukatar a dakatar da ayyana zabar Kenyatta da aka yi bisa dalilan tabka magudi a zaben.
Gungun kawancen jam'iyyun sun kuma bayyana cewa, hukumar zaben ta tilasta wa wasu ma'aikatan zaben su canja alkaluman zaben, yayin da aka bukaci wakilan jam'iyyu su sanya hannu kan wasu sabbin takardun sakamakon zabe, ko da yake babu wani martani kan hakan daga hukumar zaben.
Har ila yau, kawancen jam'iyyun sun yi korafin cewa, ko a ranar Litinin, hukumar zaben ta kira wasu wakilan jam'iyyu, da su zo su gyara wasu kura-kurai a takardunsu, matakin da suke bayyanawa a matsayin wata dabara ta tabka magudi.
Don haka sun bayyana cewa, a shirye suke su gabatar da kukansu a gaban kotun kolin kasar.
Sai dai masu sa-ido na gida da waje da suka kalli yadda zaben ya gudana a kasar ta Kenya, sun bayyana cewa, an gudanar da zaben cikin lumana da kuma adalci.(Ibrahim)