A gun taron, an sanar da wasu 'yan wasa da masu horarwa da su shiga jerin sunayen 'yan wasa mafi shahara a Afirka, ciki har da dan wasan iyo wato nunkaya daga kasar Afirka ta kudu ,mai sunan Penelope Heyns, dan wasan kwallon kafa daga kasar Kongo Francois Mpele, mai bada horo ta fannin fasahar wasan kwallon kafa daga kasar Aljeriya Rabah Saadane, da kuma jami'in kula da wasanni daga kasar Cote- D'Ivoire Lassana Palenfo.
Wakilai fiye da dari daya sun halarci taron, inda suka saurari jawabai game da muhimmiyar rawar da fasahohi suka taka wajen inganta sha'anin wasanni a Afirka.Bugu da kari, memba a kwamitin kula da harkokin wasanin Olympics na kasar Zambia Patrick Chamunda, da takwarorinsa na kasar Poland da Jamus su ma sun halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.
An gudanar da taron bisa kan tallafin da hukumar hadin gwiwa ta wasannin Olympics ta Afirka da kuma kwmaitin kula da wasannin Olympics ta kasar Mali, kana ATP na daya ne daga cikin kafofin watsa labaru da suka bayar da labarai game da wannan taro.(Zainab)