in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron koli na majalisar wasanni ta Afirka a karo na 43
2012-03-14 09:18:41 cri
Bisa labarin da aka bayar a kwanakin baya, an ce, za a gudanar da taron koli na majalisar wasanni ta Afirka a karo na 43 tun daga ranar 14 zuwa ta 17 ga wannan wata a birnin Asmara na kasar Eritrea.

Bisa labarin da shugaban sashen kula da harkokin wasanni na kasar Eritrea ya bayar, wakilai 186 daga kasashe 54 na Afirka za su halarci taron, ciki har da ministoci da jami'an kula da wasanni da dai sauransu. Bisa shirin da aka yi, membobin kwamitin gudanarwa za su halarci taron da za a yi daga ranar 14 zuwa ta 15, kuma dukkan wakilai za su halarci taron da za a yi a ranar 17 ga wannan wata. A ranar 16, za a kai dukkan wakilai zuwa wurare na yawon shakatawa da na tarihi don yin ziyara da kasha kwalkwatar ido.

Tsohon sunan majalisar wasanni ta Afirka, shi ne kwamitin wasanni na Afirka, wanda aka kafa a birnin Brazzaville na kasar Kongo a shekarar 1965, kuma an canja sunan a shekarar 1976.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China