in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin hanci da rashawa na yi wa harkar wasannin kasar Indiya tarnaki
2012-12-22 18:38:59 cri
Cin hanci da rashawa matsala ce dake addabar kasashe masu tasowa da yawa. A yau za mu leka kasar Indiya, mu dubi yadda wannan matsalar ke yi wa harkar wasannin kasar tarnaki.

A farkon watan Disamba, kwamitin Olympics na kasa da kasa ya yanke shawarar dakatar da wakilcin kasar Indiya, sabo da yadda aka yi magudi a zaben shugabannin kungiyar Olympics din kasar. An ce sabon shugaban kungiyar Olympics ta Indiya Abhay Singh Chautala, da babban sakataren kungiyar Lalit K. Bhanot, dukkansu sun samu mukamansu ne ba tare da takara da wani ba, abin da ya sa ake ganin cewa babu adalci a cikin zaben nasu.

Kafin dai wannan batu, tsohon shugaban kungiyar Olympics ta kasar Indiya Suresh Kalmadi, ya yi murabus bayan da aka kama shi da laifin hadiye makuden kudin jama'a. Kana sabbin shugabannin kungiyar da aka nada an ce suna da alaka ta kut da kut da wannan mutum, wadanda su ma ake tuhumarsa da aikata laifi.

Ga misali, Abhay Singh Chautala, wanda ke jagorantar kungiyar Olympics ta kasar Indiya a yanzu, ya taba zama shugaban kungiyar wasan dambe na kasar. A shekarar 2010, an gano yana ajiyar makuden kudi a banki, wanda yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 25. Har kuma izuwa yanzu Chautala ya kasa ba da amsa mai gamsarwa ga tambayar da aka yi masa cewa daga ina ya samu kudi da yawa haka. Haka kuma, kungiyar wasan dambe ta kasa da kasa ita ma ta dakatar da wakilcin kasar Indiya, bisa zargin cewar ba a nuna adalci ba yayin da ake zaben shugaban kungiyar wasan dambe ta kasar.

A nasa bangare, babban sakataren kungiyar Olympics ta Indiya, Lalit K. Bhanot, ya taba zama daya daga cikin manyan jami'ai masu kula da taron wasannin kasashen renon Ingila na shekarar 2010. Ana zarginsa da aikata zamba wajen ba wa wani kamfanin gini na kasar Swizterland damar kula da wasu ayyukan gini, a karkashin aikin shirya taron wasannin kasashen renon Ingila, batun da ya haddasa asarar kudin da yawansu ya kai dala miliyan 18. Sakamakon batun, an jefa Bhanot cikin kurkuku, inda ya kwashe watanni 11 yana zama a can, har zuwa lokacin daya samu belli a watan Janairun bana.

Ina dalilin da ya sa ake yawan samun cin hanci da rashawa a fagen wasannin motsa jiki na kasar Indiya? Jaridar 'Daily Post' ta kasar ta bayyana cewa, jami'ai masu kula da harkar wasanni da yawa sun kasance 'yan siyasa ne. Kamar su Abhay Singh, da Lalit K. Bhanot dukkansu sun kasance manyan kusoshi ne a jam'iyyar Indian National Congress dake mulki a kasar.

Hakika, a kasar Indiya, siyasa ta dade tana yin tasiri kan harkar wasanni, domin 'yan siyasa da yawa na kokarin neman kudi ta karkashin ayyukan wasanni. Ga misali, Suresh Kalmadi ya yi shekaru 16 yana kula da kungiyar Olympics, yayin da Vijay Kumar Malhotra mai shekaru 80 ya yi kusan shekaru 30 yana rike da mukamin shugaban kungiyar wasan harbi, kuma sun samu damar dadewa kan mukaman nasu ne, sakamakon rashin wasu 'yan takara dake shiga zaben tare dasu.

Hanyoyi da dabaru da wadannan 'yan siyasa suke yin amfani da su wajen neman kudi daga harkar wasanni suna ba mutane mamaki. Ga misali, a lokacin da kasar Indiya ke karbar bakuncin taron wasannin kungiyar kasashen renon Ingila, Mista Suresh Kalmadi ya kasance shugaban shirya taron, wanda ke yanke shawara kan wa zai samu damar kula da ayyukan gini da yawa. Bayan da aka kammala taron, an gano abubuwan kunya, ga misali, 'toilet paper' takarda mai laushi da ake amfani da ita a bayan gida an sayo ko wane gammo guda kan kudi Naira 10,675 a maimakon darajar ta da bata wuce Naira 60 ba, sa'an nan kwalaba mai dauke da ruwan wanke hannu wadda darajar kowace bata wuce Naira 300 an saye ta Naira 9500 ko wacce. Baki daya an ce kashi 1 daga cikin kashi 6 na kudin da gwamnati ta ware don gina dakunan wasanni ya zama toshiyar baki, da aka baiwa jami'ai masu kula da taron. Irin wannan cin hanci da rashawa ya sa an samu matsaloli da yawa a yayin taron wasannin, inda kayayyakin amfani da yawa sun lalace, har ma wani dakin wasa ya rushe kafin a fara wasanni a ciki.

Cin hanci da rashawa ya kasance babbar matsala da za ta iya shafar fannoni daban daban na al'umma, don haka harkar wasannin motsa jiki ita ma musamman a wannan kasa ta samu koma baya sakamakon matsalar cin hanci. Muna fatan mahukuntan kasashe daban daban za su nuna sanin ya kamata, su yi kokarin hana siyasa shiga cikin harkar wasanni, tare da gudanar da ayyukan wasannin a bayanne, domin jama'a su iya ganewa idanun su yadda komai ke wakana, ta yadda za a samu damar tabbatar da ci gaban harkar wasanni, gami da kyakkyawar zamantakewar al'umma.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China