in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta yi kira da a daina kazamin fada a filin wasa
2010-09-15 08:54:34 cri

Masu sauraro, a ran 29 ga watan Mayu na shekarar 1985, wani hargitsin da ya janyo kashe-kashe mai tsanani ya faru a filin wasan Heysel na birnin Brussels a kasar Belgium a yayin gasar dake tsakanin kungiyar Liverpool da ta Juventus, a sanadin haka, mutane fiye da goma sun rasa rayuka, hakan ya sa jama'ar kasa da kasa musamman ma masu sha'awar wasan kwallon kafa da kungiyoyin wasan kwallon kafa da kamfanonin da abin ya shafa suka yi hasara mai tsanani. Yanzu a kasar Sin, ma haka abin yake, wato keta ya kan bayyana a filin wasan kwallon kafa, misali, malaman horas da 'yan wasa su kan shiga filin wasa kamar yadda suke so a yayin gasa, da 'yan wasa su kan yi kazamin fada a tsakaninsu, da masu sha'awar wasan kwallon kafa sun tarwatsa mota har 'dan wasa ya ji rauni a ido, da 'yan wasa ko masu sha'awar wasan kwallon kafa su kan yi fada a tsakaninsu, sakamakon rashin kasancewa cikin shiri yadda ya kamata.

Kan wannan batu, direktan kwamitin binciken horo na hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sin Wang Xiaoping ya yi kira da kakkausar murya cewa, "Wasan kwallon kafa a kasar Sin takarar fasahar wasa ne, ba wasan dambe ba ne."

Wang Xiaoping ya ci gaba da cewa, "Yanzu wasu hargitsi sun sake faruwa a yayin gasar wasan kwallon kafa da aka yi a kasar Sin, wadda hakan ya kawo mugun tasiri ga muhallin wasan kwallon kafa da bunkasuwarsa, wasu shugabannin kungiyoyin wasan kwallon kafa da malaman horas da 'yan wasa da 'yan wasa sun saba ka'idojin da aka tanada musamman ma domin gasar sana'a a kasar Sin wadda har sun zargi alkalan wasa a filin wasa, wasu kuwa sun bugi alkalan wasa a yayin gasa. A wasu filayen wasa, aikin kiyaye zaman lafiya bai gudana yadda ya kamata ba, an tarwatsa motoci har wasu 'yan wasa da masu sha'awar wasan kwallon kafa sun ji rauni, duk wadannan laifuffuka ne da suka janyo rashin samun kwanciyar hankalin zamantakewar al'umma. Idan ba a hana wadannan laifuffuka cikin lokaci, to, hargitsi mai tsanani zai faru."

Wang Xiaoping ya kara da cewa, nan gaba za a hori masu laifi bisa doka, ya ce, dalilin da ya sa haka shi ne domin masu aikin gudanar da wasan kwallon kafa ba su kwarre da aikinsu ba, kuma matakan gudanar da wasan kwallon kafa ba su da inganci sosai, ban da wannan kuma wasu masu sha'awar wasan kwallon kafa sun mayar da filin wasa a matsayin wurin nuna bakin cikinsu, kazalika, abu mafi muhimmanci shi ne kamata ya yi masu aikin wasan kwallon kafa kamarsu shugabannin kungiyoyi da malaman horaswa da 'yan wasa su daga matsayinsu daga dukkan fannoni musamman wajen matsayin sana'a. Game da batun kula da masu sha'awar wasan kwallon kafa, Wang Xiaoping ya ce, yanzu masu sha'awar kwallon kafa na kasar Sin suna fatan matsayin wasan kwallon kafa na kasar Sin zai kai matsayin koli a duniya nan take, amma ba mai yiyuwa ba ne a cim ma wannan buri cikin gajeren lokaci, shi ya sa, ya fi kyau a kara mai da hankali kan aikin kula da masu sha'awar kwallon kafa. Ana iya cewa, duk wadannan sun hana bunkasuwar wasan kwallon kafa a kasar Sin.

To, ta yaya za a warware wadannan matsaloli? Wang Xiaoping ya ba da shawara cewa, da farko, ya fi kyau a shirya wani taron kara wa juna sani tsakanin hukumar kiyaye kwanciyar hankali ta kasar Sin da kwamitin yanke shawara da kwamitin binciken horo na hukumar kula da wasan kwallon kafa ta kasar Sin da alkalan wasa da 'yan wasa da manyan shugabannin kungiyoyin wasan kwallon kafa da wakilan kafofin watsa labarai da wakilan masu sha'awar wasan kwallon kafa da dai sauransu ta yadda za su ba da shawarwari kan batun yadda za a hori ayyukan sabawa ka'idoji da dokokin da abin ya shafa. Daga baya kuma, ya kamata a gyara ka'idojin horo na yanzu. A karshe dai, ya fi kyau a tsara wata doka ta takarar sana'a bisa halin da wasan kwallon kafa ke ciki a kasar Sin yanzu, bayan haka, halin da masu aikin wasan kwallon kafa ke ciki zai samu kyautatuwa a kai a kai.

To, masu sauraro, yanzu bari mu kara karanta muku wani bayani na musamman game da wasannin zamani iri biyar. Kamar yadda wata kila kuka sani, wasannin zamani iri biyar sun hada da wasanni iri biyar wato wasan takobi da wasan sukuwar dawaki da wasan harbe-harbe da wasan ninkaya da kuma wasan gudun kewaye gari.

A ran 7 ga wata na bana, aka rufe gasar cin kofin duniya ta wasannin zamani iri biyar a karo na 50 a birnin Chengdu na lardin Sichuan na kasar Sin, wannan karo na farko ne da aka shirya wannan babbar gasa a kasar Sin, 'yan wasan da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 30 sun halarci wannan gasa.

Cibiyar wasa ta wasannin zamani iri biyar ta shekarar 2010 tana gundumar Shuangliu ta birnin Chengdu na lardin Sichuan. Yanzu ana kiranta da sunan "cibiyar wasa ta wasannin zamani iri biyar ta Coubertin", a cikin wannan cibiyar, an gina dakin wasan ninkaya da na wasan takobi da filin wasan sukuwar dawaki a wajen daki da filin wasan harbe-harbe da guje-guje da kuma cibiyar watsa labarai. Shugaban babbar hukumar kula da wasannin zamani iri biyar ta kasa da kasa Klaus Schumann ya bayyana cewa, wannan cibiya ta kai matsayin koli a duniya, yanzu, biranen Beijing da Chengdu da Guangzhou sun riga sun zama cibiyoyin horas da 'yan wasannin zamani iri biyar uku sun kasance mafi muhimmanci a kasar Sin. Schumann shi ma ya taba bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta zama cibiyar wasannin zamani iri biyar a nahiyar Asiya.

A yayin wannan gasar cin kofin duniya ta wasannin zamani iri biyar da aka yi a birnin Chengdu na kasar Sin, 'dan wasa Cao Zhongrong ya samu damar kasancewar na hudu a bangaren maza a yayin gasar, amma sauran 'yan wasan kasar Sin ba su samu sakamako mai gamsarwa ba. Game da wannan, mataimakin direktan cibiyar kula da wasan takobi da tseren keke ta babbar hukumar kula da wasan motsa jikin kasar Sin Xu Haifeng ya bayyana cewa, akwai matsala a gaban 'yan wasan kasar Sin, ko a fannin fasahar wasa, ko a fannin dabarar horaswa, kuma wasannin zamani iri biyar sun riga sun shiga ayyukan gasa na gasar wasannin Asiya da za a yi a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin a watan Nuwamba na bana, 'yan wasan wasannin zamani iri biyar za su yi takara domin neman samun zakaru hudu a yayin gasa, Xu Haifeng ya ce dole ne 'yan wasan kasar Sin su samu zakara a yayin gasar wasannin Asiya.(Jamila Zhou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China