in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lionel Messi ya sake zama gwarzon dan kwallon duniya na shekara ta 2012
2013-01-11 16:40:18 cri
Lionel Messi ya sake zama gwarzon dan kwallon duniya na shekara ta 2012, Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA ce dai ta bayyana hakan bayan tantance 'yan takarar wannan lambar yabo ta Ballon d'Or, wadda ake baiwa dan wasa mafi hazaka a kowace shekara. Wannan shi ne karo na 4 da Messin dan kasar Argentina kuma dan kungiyar Barcelona ya samu kyautar a jere wato tun daga shekarar 2009 zuwa 2012.

Yayin bikin karbar lambar girmamawar da ya gudana a birnin Zurich, Messi ya godewa dukkanin wadanda suka tallafa masa wajen samun wannan nasara, ciki hadda 'yan wasan kulaf din sa na Bacerlona, da kocin sa, da kuma dukkanin masu yi masa fatan alheri. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China