Hakazalika kuma, ministan kula da harkokin wasanni na kasar Zimbabwe David Coltart, ya yi tir da wannan lamari, da ma duk wani irin harin ta'addanci wanda ke kawo barazana ga jama'a. Bugu da kari an nuna rashin amincewa da irin wannan hari da aka kaiwa gasar motsa jiki, wadda bata da nasaba da siyasa ko kadan.
Har ila yau, kafofin watsa labaru na kasar Kenya sun bada sharhi cewa, kungiyar 'yan wasan kasar Kenya ta ci nasara a gasar gudun yada-kanin-wani ta mata a birnin Boston, sai dai sa'a daya da hakan ne fashewar boma-bomai ta auku, lamarin ya maida gasar tamkar wani bala'i, don haka dai jama'a, ba za su iya kawar da damuwar da wannan lamarin ya kawo daga zuciyarsu cikin kankanin lokaci ba. (Zainab)