in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bom da aka kai a wani masallacin Siriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43
2013-03-22 15:42:11 cri

A ranar 21 ga wata da dare, an kai harin kunar bakin wake a masallacin Iman da ke birnin Damascus hedkwatar kasar Siriya, kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43, cikinsu har da wani shahararren shehu malami na addinin Musulunci na kasar.

Harin da ya abku ne a yayin da ake gudanar da wani bikin addini a cikin masallacin, a karkashin shugabancin fitaccen shehu malami mai martaba a kasashen da ke bin addinin Musulnci, Mohammad Said Ramadan al-Bouti. Haka kuma, Bouti ya taba nuna adawarsa karara ga bangaren 'yan adawar kasa masu tsattsauran ra'ayi, kuma ya taba yin kira ga masu bin addini na Siriya da su nuna goyon baya ga sojojin gwamnatin don yaki da dakaru dake adawa da gwamnatin kasar.

Bayan da aka samu fashewar bom, gwamnatin Siriya da masu bin addini sun ba da sanarwa, inda aka bayyana cewa, 'yan ta'adda daga cikin bangaren adawa na kasar sun kai wannan harin bom, haka kuma kafofin yada labaru na kasar sun bayyana cewa, dalilin da ya sa aka kai harin shi ne don hallaka Bouti.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China