in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun rasu sakamakon wani harin bam a Nigeria
2013-02-21 09:49:53 cri

Rundunar sojin Nigeria reshen jihar Borno ta tabbatar da rasuwar mutane 3, yayin da wasu 2 kuma suka jikkata, sakamakon wani harin bam da wani wanda ba a san ko wane ne ba ya aiwatar a garin Maiduguri na jihar ta Borno, dake arewa maso gabashin Nigeria.

A cewar kakakin rundunar hadin gwiwar jami'an soji da 'yan sanda dake jihar kanar Sagir Musa, maharin wanda ake zaton dan kungiyar nan ta Boko Haram ne, ya yi yunkurin kai harin ne kan wata tawagar jami'an tsaro dake sintiri a kan wani shataletale dake birnin na Maiduguri, kafin bam din da yake dauke da shi ya tashi, ya kuma hallaka shi tare da karin wasu mutane 2.

Kanar Musa wanda bai yi karin bayani kan lamarin ba, ya ce, harin ya shafi wata motar jami'an tsaro guda daya, yayin da kuma tuni aka rankaya da wadanda suka samu raunika zuwa asibiti.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China