in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana zaman dar-dar a Kaduna da ke arewacin Najeriya bayan harin bom
2013-03-20 10:12:54 cri

An yi zaman dar-dar a jihar Kaduna da ke arewacin kasar Najeriya ranar Talata bayan harin bom da aka kai kan wata babbar motar fasinja da za ta tafi Lagos, inda harin ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 20, kana wasu da dama suka jikkata.

An baza sojoji da 'yan sanda a cikin garin don kwantar da hankalin jama'a da kuma kawar da duk masu yunkurin tada kayar baya.

A unguwar Barnawa dake kudancin jihar, an gano sojoji da dama dake jiran ko ta kwana.

Haka ma a yankin arewacin birnin, jami'an tsaro suna tsai da mutane suna binciken su a kan hanya, yayin da kuma aka ajiye sojojin sama dauke da makamai a hanyar zuwa garejin Mando.

Bugu da kari, jami'an tsaro sun yi ta sintiri a kan titin Ahmadu Bello har zuwa sassan kudancin jihar, da kuma a unguwannin garejin talbijin, sabon tasha da kuma gidan waya.

Sauran jami'ai masu sintiri suna zagaye a arewacin jihar a wurare da suka hada da unguwar Sarki, unguwar Shanu da unguwar Kawo.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China