in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ruwanda ya yi kiran hadin kan Afirka
2013-04-17 09:57:09 cri

A ranar Talatar nan, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bukaci 'yan Afirka da su yi aikin bunkasa hadin kai da dunkulewa waje guda tsakaninsu.

Shugaban ya yi wannan kira ne yayin da yake jagorantar zaman taron majalisar dokokin gabashin Afirka (EALA), wanda ke gudanarwa a ginin majalisar dokokin kasar Ruwanda, dake babban birnin kasar, Kigali.

Kagame ya bayyana wa 'yan majalisu da suka taho daga kasashen Burundi, Kenya, Ruwanda, Tanzaniya da Uganda cewa, hadin kai da dunkulewa waje guda a Afirka shi ne muhimmin abu a fuskar cimma burin taka muhimmiyar rawa a fagen duniya. Ya ci gaba da cewa, har izuwa wannan lokaci, a Afirka ne kadai ake wa jama'a gargadi, dangane da abin da ka iya biyo bayan irin zabi da suka yi na demokuradiyya.

Shugaban ya yi kira musamman ga yankin gabashin Afirka da ma nahiyar baki dayanta, da ta fito a fafata da ita a fuskar hada-hadar cinikayya da zuba jari a cikin Afirka.

Ya ce, a nahiyar Afirka ne kadai ake karya dangane da jama'a, sannan a hana kai 'yancin mai da martani, wato a bangaren wadanda ke koyar da dacewar 'yancin bayyana ra'ayi ke nan.

Da kuma ya tabo manufofin kasashen yammacin duniya wadanda ba su da dadi ga Afrika, Kagame ya ce, ya dace nahiyar ta tashi tsaye ta dage kan 'yancinta.

Shugaban ya yi kira ga kasashen Afirka da su rage dogaro da kafofin raya tattalin arziki daga waje, wadanda ci gabansu ba shi da tabbas.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China