in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afirka ta Kudu ya sanar da kawo karshen aikin tawagar kasarsa a CAR
2013-04-11 10:03:04 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sanar a ranar Laraba da kawo karshen aikin tawagar sojojin kasar Afrika ta Kudu a Afrika ta Tsakiya (CAR).

A cewar kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, mista Mac Maharaj, shugaba Zuma ya yi wannan furuci a lokacin da yake sanar da majalisar dokokin kasar kan batun janye sojojin Afrika ta Kudu dake Afirka ta Tsakiya.

'Afrika ta Kudu ta janye sojojinta bayan ganin yanayin tsaro ya kara tabarbarewa a CAR da ganin kuma babu wata halatattar gwamnati.' in ji Maharaj.

Yan adawa na zargin shugaba Zuma da batar da 'yan majalisa da al'ummar kasa kan tura sojojin Afrika ta Kudu a Afrika ta Tsakiya, ko da yake Zuma ya tabbatar da sahihancin aikin a wannan kasa dake tsakiyar Afrika bisa tushen yarjejeniyar soja da aka sanya kanta tare da gwamantin Afrika ta Tsakiya a shekarar 2007.

A cewar wannan yarjejeniya, Afrika ta Kudu za ta samar da horo ga rundunar sojojin kasa da kuma sojojin musammun na Afrika ta Tsakiya da kuma taimakawa kasar gyara gine-ginen soja na Bouar da Bangui. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China