A ranar Lahadin nan ne shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame da takwaransa na jamhuriyar Congo Denis Sassou-Nguesso suka yi kira ga masu tawaye a yankin gabashin jamhuriyar demokradiyar Congo(DRC) da su kiyaye matsaya da aka cimma a taron kolin kasashen yankin Great Lakes(LCGLR) wanda aka yi a birnin Kampala.
Shugaba Sassou-Nguesso ya isa kasar Ruwanda ne a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka bayar, shuwagabannin biyu sun yaba matsayar da shuwagabannin kasashen yankin Great Lakes(LCGLR) suka cimma a taron kolin da suka yi a birnin kampala.
Shugaba Sassou-Nguesso ya isa kasar Ruwanda ne don yin ziyarar aiki ta kwanaki biyu bisa gayyatar takwaran nasa, inda shuwagabannin biyu suka yi shawarwari kan dangantaka tasakanin kasashen nasu, da kuma batutuwa da suka shafi yankin da ma duniya baki daya, tare da nuna gamsuwa kan karin dankon hadin kai a fuskar siyasa da hadin gwiwa tsakanin kasar Ruwanda da jamhuriyar Congo.
Sanarwar ta bayyana cewa, shuwagabannin biyu sun yi shawarwari sosai kan rikicin da ake fama da shi a gabashin jamhuriyar demukradiya Congo (DRC) inda kuma suka yi na'am da matsayar da aka cimma a taron kolin kasashen yankin Great Lakes (LCGLR) da aka yi a birnin kampala.
Yayin taron nasu a birnin Kampala, shuwagabannin na LGCLR sun yi kira ga 'yan tawayen M23 da su janye dakarunsu da a kalla nisan kilomita 20 daga yankin arewacin birnin, wanda dakarun wadanda sojoji ne da suka yi bore a cikin watan Aprilu, suka kwace ranar Talata.
Sanarwar hadin gwiwar na mai bayyana cewa, suna kira ga gwamnatin jamhuryar demokradiyar Congo(DRC) da 'yan tawayen M23 da su sadaukar da kai wajen aiwatar da matsayar da aka cimma a birnin kampala domin kyakyawar dama ce ta warware rikicin.(Lami)