in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ruwanda ta ki amincewa da zargin yin kawance da dakarun adawar Kongo(Kinshasa)
2012-12-14 11:48:33 cri

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana a ran 13 ga wata, yayin babban taron tattaunawa karo na 10 da aka yi a babban birnin kasar Kigali cewa, gwamnatin kasarsa ba ta taba yin kawance da dakarun adawar Kongo(Kinshasa) ba, kuma ba ta tsoma hannu cikin harkokin kasar.

A cikin watan Afrilu na shekarar bana, wasu hafsoshi da sojoji masu goyon bayan majalisar kare 'yancin jama'ar kasar Kongo(Kinshasa), sun gudanar da juyin mulkin a kasar, inda suka kafa sabuwar kungiyar adawa da gwamnatin kasar ta M23, kuma a ran 20 ga watan Nuwanba, kungiyar adawa ta M23 ta sanar da mamaye yankin Goma, cibiyar lardin Nord-Kivu da ke gabashin kasar.

MDD da wasu kasashen yamma sun zargi kasar Ruwanda da goyon bayan kungiyar adawa ta M23, musamman a fagen yaki da sojojin gwamnatin kasar ta Kongo(Kinshasa). Duk dai da cewa, gwamnatin kasar ta Ruwanda na ci gaba da musanta wannan zargi, don gane da hakan, kasashen Jamus, da Burtaniya da kuma bankin duniya sun dakatar da taimakon kudi ga kasar tun cikin watan Mayu na shekarar da muke ciki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China