Bisa sanarwar da fadar shugaban kasar Faransa ta bayar, an ce, a safiyar ranar 6 ga wata, wani sojan Faransa ya mutu a cikin aikin sojan da aka dauka a gabashin kasar Mali. A sabili da haka, yawan mutuwar sojojin Faransa ya karu zuwa hudu.
A ranar Alhamis 7 ga wata, ministan tsaron kasar Faransa ya kai ziyara a Mali ba zato ba tsammani, domin karawa sojojin kasar kwarin gwiwa, inda ya bayyana ra'ayin kasar Faransa na taimakawa jama'a da kasar Mali wajen mayar da ikon mulkin kasar, tare da yin shelar cewa, ayyukan rundunar sojan Faransa za su kammala yadda ya kamata.
A sa'i daya kuma, shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya bayyana cewa, za a janye sojojin Faransa daga watan Afrilu na bana, a maimakon watan Maris.
Wani masanin aikin soja na Faransa ya yi nazarin cewa, watakila za a sake tsawaita wa'adin aikin soja da Faransa ke yi a kasar Mali, har ma zuwa watan Yuli, sabo da babu wata masaniya kan hakikanin yawan dakaru masu tsattsauran ra'ayi na kungiyar Musulmi.(Fatima)