Yayin ziyarar Jean-Yves Le Drian, ya nuna cewa, tun ranar 11 ga watan Janairu, kasar Faransa ta tsai da kudurin dukufa wajen ba da taimako ga kasar Mali kan yakin neman mulkin kan kasa da jama'arta, zuwa yanzu kuma, kasar Faransa ba ta taba nuna wata shakka kan kudurin ba ko kadan.
Ya ce, kasar za ta ci gaba da taimakawa kasar Mali tare kuma da nuna juyayi da girmamawarsa ga sojojin Faransa guda 4 wandanda suka rasu yayin rikici.
Bisa labarin da aka samu, ran 6 ga wata da dare, shugaban kasar Faransa ya sanar da sabon shirin janye sojojin kasar daga kasar Mali.
Kasar Faransa za ta fara janye sojojinta daga kasar Mali a watan Afrilu, kuma sojojin kasar za su dauki matakin karshe na aikacen aikacen soja a kasar Mali a watan Maris.
Ran 7 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya sake sanar da wannan shirin. Yayin wani intabiyu na talabijin, ya nuna cewa, gaskiya ne, kasar Faransa za ta janye sojojinta daga kasar Mali a watan Afrilu, amma ba za a janye dukkan sojojin kasar daga kasar Mali cikin kwana guda ba, wato dai bi da bi ne za a janye su.
Ya kuma jadadda cewa, tun da farko kasar Faransa ta tabbatar da cewa, ba za ta yi ajiyar soja na dindindin a kasar Mali ba. (Maryam)